Labarai
Dalilan da suka sanya mu ficewa daga Najeriya – ShopRite
Hukumar gudanarwar kantin ta yanke shawarar fara sayar da dukkanin hannayen jari, ko kuma mafi yawa daga cikinsa, ga ‘yan kasuwa.
Shararren kantin na ShopRite mallakin kasar Afirka ta kudu ya sanar da cewa ya fara gudanar da wani tsari da zai bashi damar dakatar da dukkanin ayyukansa a kasar.
ShopRite Holdings Limited ya ba da sanarwar a ranar Litinin a cikin rahoton hadar-hadarsa na shekara wanda ya kare a ranar 28 ga Yunin, 2020.
Kantin, wadanda ya sanar da samun karin kashi 6.4 cikin dari na ribar da ya samu duk da kalubalen da annobar Covid-19 ta haifar, y ace ya dauki matakan dakatar da ayyukansa a Najeriya. “Sakamakon bukatar hakan daga masu zuba jari daban-daban, hakan ta sanya muka bullo da wannan matakin Najeriya.”
Duk da cewa kantin na iya samun karin wani kaso na musamman na hada-hadarsa, sai dai abun ba haka yake ba akasar Afirka ta Kudu. A cewar rahoton, hadar-hadar tsagin kantin da ke wajen kasar amma ciki banda Najeriya sun samar da kashi 11.6 cikin dari na ribarsa, ko da yake an samu faduwar riba da kaso 1.4. Kantin ya danganta wannan koma baya da dokar kullen da aka samu a wasu kasashen Afirka da dama sakamakon barkewar annobar Coronavirus.
You must be logged in to post a comment Login