Labarai
INEC ta yi gaggawar bayyana zaben Kano a matsayin inconclusive- APC
Jama’iyar APC, ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayyana sakamakon zaben gwamnan Kano da aka gudanar ranar 18 ga wannan watan da muke ciki na Maris a matsayin wanda da bai kammala ba.
Lauyan da ke bai wa jama’iyar ta APC shawara kan harkokin shari’a Barisata Abdul Fagge ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da jam’iyyar ta gudanar a ofishin yakin neman zaben APC da ke kan titin club Road.
A cewar lauyan, an samu rikice-rikice tare da soke kuri’un da aka kada a wasu akwatun yayin zaben.
Barista Abdul Fagge, ya kara da cewa jama’iya ta APC za ta bi matakin doka domin ganin an sake zaben a wurarren da aka samu matsala.
A nasa bangaren, mataimakin gwamnan Kano kuma dan takarar gwamna a zaben na bana Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce, jam’iyyar ta APC ta yi nazari sosai a kan abubuwan da suka faru a kan zaben tare da shiin daukar matakin doka don bin kadun al’ummar jihar Kano da suka kada musu kuri’a.
Gawuna, ya kara da cewa za su zuba ido a kan matakin shari’ar tare da karbar duk hukuncin da ubangiji ya ya zartar.
Haka kuma dan takarar gwamnan, ya ja hankalin al’ummar jihar Kano da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda tare da rungumar tsarin zaman lafiya.
Rahoton: Abba Isah Muhammad
You must be logged in to post a comment Login