Labaran Kano
Ya kamata shugaba Buhari ya sake duba batun rufe boda
Wata kungiyar ‘yan kasuwar Arewa wadanda mambobinsu ke harkar tufafi sun koka ga yadda suke asarar miliyoyin kudade sakamakon rufe boda da gwamnati tarayya tayi.
Shugaban kungiyar Abubakar Kabir Babawo ne ya bayyana haka jiya a yayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyar da za’a magance wannan matsala.
Jaridar Kano Focus ta rawaito cewar a ranar 19 ga Augustan watan da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta rufe dukkanin iyakokin da suka hade da Najeriya domin magance matsalolin shigo da kayayyakin abinci kamar su shinkafa a wasu lokutan ma har da makamai.
Wannan sabon tsari wanda aka yi wa lakabi da Ex-Swift yunkuri ne da gwamnatin Najeriya da hukumar kwastam, da hukumar shige da fice ta kasa da ‘yan sanda da sauran jami’ar tsaro suka fito da shi.
Mal Babawo ya bukaci shugaba Buhari da ya sake duba batun rufe iyakokin da aka yi ta hanyar saukakawa ‘yan kasuwa, duba da matsanacin hali da ‘yan kasuwa ke ciki a yanzu.
Ya ce kawo yanzu ‘yan kasuwa na cikin halin kunci da takura duba da irin asarar miliyoyin kudade da suke fuskanta .
Ya ce abin takaici ne yadda wasu ke baiwa shugaban kasa shawarar da bata dace ba dangane da rufe iyaka da ya danganci kasar da sauran makwabtan kasasashen Afirka.