Labarai
Za mu yi wa Kotu biyayya kan zargin zabtarewa ma’aikata kudi – Ganduje
Gwamnatin Kano ta ce, zata yi biyayya ga hukuncin Kotu bayan da kungiyar ma’aikatan Kotuna ta gurfanar da ita a gaban babbar kotun jihar Kano, kan batun zabtare musu albashi.
Kwamishinan Sharia kuma Atoni janar na Kano Barista Lawan Abdullahi Musa ne ya bayyana hakan a ya yin zantawarsa da manema labarai anan Kano.
Barista Lawan Abdullahi ya ce babu gudu ba ja da baya akan yunkurinta na gyara duk wasu gidaje ko filaye mallakin gwamnati wadanda ba’a amfani dasu a ko ina suke domin sake ingantasu ta yadda zasu rika samarwa da gwamnati kudaden shiga.
Kwamishinan Shari’ar ya kara da cewa, ya yi mamaki yadda kungiyar ma’aikatan kotu suka gurfanar da gwamnati a gaban babbar kotun Kano kasancewar suna da masaniya kan yadda tsarin shigar da kara wadda ta shafi al’amuran albashin ma’aikata yake da shi, amma suka gurfan ar da gwamati a gaban kotun.
Labarai masu alaka :
Gamayyar kungiyoyin kwadago ta yi barazar gurfanar da Ganduje a Kotu
Kotu ta dakatar da Ganduje daga ciyo bashi
Bude kotun daukaka kara a Kano zai bunkasa harkokin shari’a- Barrister Abdul Fagge
Kotu ta saki Naziru Sarkin waka
Haka kuma kwamishinan ya ce kotun da’ar ma’aikata ce kadai ke da hurumin sauraron karar da kungiyar ma’aikatan Kotuna suka shigar a babbar kotun jiha kan batun zabtare musu albashi da gwamnati ta yi.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya rawaito cewa Barista Lawan Abdullahi na cewa gwamnatin Kano ta sauyawa kamfanin buga jarida na TRIUMPH guri zuwa rukunin gidaje na SheiIkh Isyaka Rabiu domin cigaba da gudanar da ayyukansu a can.
You must be logged in to post a comment Login