Labarai
Ba yanzu za a bude tashoshin jiragen kasa ba – gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta ce dole ne ayi amfani da matakan kariya kan cutar Covid-19 da zarar an bude tashoshin jiragen kasa.
Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce babu wani fasinja da za a yarje masa shiga jirgin kasa matsawar, ya ki amfani da dokokin da aka gindaya da suka kunshi amfani da safar rufe hanci da baki.
Ministan wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ya ce ma’aikatarsa bata shirya bude tashosin jiragen kasa ba a nan kusa.
We’re not in a hurry to start train operations because of the danger of covid19 spread. When we start, all health and safety protocols must apply. You will not enter a train if you don’t adhere to our rules. The train will not move if passengers do not comply.
— Chibuike.R. Amaechi (@ChibuikeAmaechi) June 20, 2020
A makon jiya ne kwamitin fadar shugaban kasa kan annobar Covid-19 ya bayyana cewa za a bude tashohin jiragen kasa, da zarar an bawa filayen jiragen sama damar fara aiki.
Jami’in gudanarwa na kwamitin Sani Aliyu ya ce za a bude tashoshin jiragen kasa da zarar, an janye dokar hana shige da fice a jihohin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login