Labarai
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe kan iyakoki
Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe kan iyakokin Najeriya na sa’o’i 24 gabanin babban zaɓen da ke tafe a ranar Asabar.
Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar kula da shige da fice ta fitar a shafinta na Twitter wanda ya samu sa hannun shugabanta, Isah Jere Idris.
Sanarwar ta ce daga gobe Asabar za a rufe dukkanin iyakokin ƙasa har zuwa ranar Lahadi 26 ga watan Feburairu.
Idris Jere ya buƙaci dukkan shugabannin hukumar da ke kan iyakoki da su tabbata an bi wannan umarni, har ma ya ce, hukumar a shirye ta ke wajen ganin ta bayar da gudummawa na ganin an gudanar da zaɓukan lami lafiya.
You must be logged in to post a comment Login