Labarai
Hukumar EFCC ta gano ma’aikatan bogi 1000 a jihar Kwara
Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa arzikin kasa ta’annati a Najeriya, ta bankado ma’aikatan bogi 1000 a jihar Kwara.
Ofishin hukumar a jihar Kwara ya bankado ma’aikatan na bogi ne a hukumar ilimin bai daya, bayan da aka gano sunayensu cikin jerin ma’aikatan da ke karbar albashi.
Da yake Magana da manema labarai a birnin Ilori, shugaban hukumar EFCC a jihar Kwara Mallam Isyaku Sharu, ya ce tasirin zaman gida dole, na daga cikin abinda ya taimaka wajen bankado ma’aikatan na bogi.
Malam Isyaku ya ce Covid-19 ta haifar da matsaloli masu tarin yawa a bangaren kiwon lafiya ba wai a Najeriya kadai ba, inda y ace ba za a kalli wannan a matsayin annoba ba, domin kuwa cin haci da rashawa itama annoba ce mai zaman kanta.
Hukumar EFCC ta ce a cikin watanni 16 ta samu nasarori da dama a jihar Kwara wajen bankado ayyukan cin hanci, ciki har da batun kwace ikon gidaje guda takwas a birnin Ilori kadai.
Malam Sharu, ya kuma tabbatarwa da al’umma cewa ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen bankado masu aikata almundahana tare da daukar matakan da suka dace a kansu.
You must be logged in to post a comment Login