Manyan Labarai
Kano:APC ta musanta zargin sauya ra’ayin kotun daukaka kara
Jamiyyar APC ta musanta zargin da jamiyyar mai hammaya ta PDP ke yi mata na yunkurin amfani alkalan da zasu saurari karar zaben gwamna daza’a gudanar a Kaduna.
Jaridar KanoFocus ta rawaito cewar idan za’a iya tunawa jam’iyyar PDP ta bayyana wannan zargi na ta ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar lahadi din da ta gabata.
Kwamishinan yada labarai Muhammad Garba ne ya bayyana zargin da jamiyyar PDP ke yi a matsayin , cewar ba gaskiya ba ce wani yunkuri ne na shafa jamiyyar APC kashin kaza domin aga baiken ta a idon al’ummar jihar Kano, tare da shafawa kotun daukaka kara laifin .
Mal Muhammad Garba a cikin sanarwa ya bayyana cewa ko a jiya litini da jamiyyar PDP ke yada wannan sanarwa mai ciki da Kazafi, kuma takan yi haka ne da zarar ta fuskanci cewar ba zata yi nasara ba .
Shariar Ganduje da Abba: Jamiyyar PDP na zargin sauya Alkalai
Ya ce APC da dan takarar ta suna da yakinin sakamakon da za’a samu bayan sauraron karar a kotun daukaka kara za’a gudanar da shi cikin adalci ne .
Ya ce gwamnatin jihar Knao ba zata yarda jamiyyar PDP ta haifar da abinda zai kawo rudani da tada zaune tsaye ba kamar yadda sanarwa ta bayyana.