Connect with us

Manyan Labarai

Shariar Ganduje da Abba: Jamiyyar PDP na zargin sauya Alkalai

Published

on

Jamiyyar PDP ta zargi jam’iyyar APC da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da  kokarin canza alkalan da zasu saurari shariar da dantakarar jam’iyyar PDP Abba Kabiru Yusuf ya shigar gaban kotun daukaka kara dake Kaduna.

 

Idan za’a iya tunawa jamiyyar PDP da dan takarar ta Abba Kabir Yusuf sun shigar da kara a kotun daukaka kara dake Kaduna , inda suke kalubalantar tabbatar da sahihancin zaben Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda mai shariah Halima Shamaki ta yanke.

 

A wata sanarwa da aka fitar a jiya da sa hannun sakataren jamiyyar Kola Ologbondiyan ,jamiyyar PDP ta kalubalanci cewar APC na bukatar alkalan da zasu iya juyawa ne domin yanke hukunci daidai da bukatar su.

Jamiyyar PDP ta bukaci ‘yan Najeriya da su halarci zaman kotun da za’a gudanar a ranar talata, wanda tun da farko aka so a gudanar da zaman a yau litiin sakamakon hutun Maulid.

Sanarwar ta kara da cewar suna da rahotannin cewar jam’iyya mai mulki da gaggan ‘’yan jam’iyya  suna kokarin gurbata alkalai da zasu saurari karar.

Sun ce jamiyar su ta samu labari daga majiya mai tushe cewar ko a goben za’a iya daga shariar har sai illa masha Allah , hakan dai zai basu damar sauya wasu daga cikin alkalan.

Sun kara da cewa tun kafin yanke hukunci dai magoya bayan gwamna suka fara nuna farin cikin su na hasashen yadda shariar zata kaya.

Idan za’a iya tunawa makamancin haka ya faru a lokacin da ake sauraron karar a kotun sauraron kararrakin zabe, a lokacin da aka canza alkalin da zai saurari karar.

Jamiyyar PDP ta gargadi duk wani canjin

Manyan Labarai

Masu Adaidaita sahu sun roki gwamnatin Kano kar ta sanya musu haraji

Published

on

Gamayyar kungiyoyin masu baburan Adaidaita sahu na jihar Kano, sun yi Kira ga gwamnatin jihar Kano, da ta sassuta musu, ko ta rage kudin harajin da ta ke kokarin sanya musu.

Mataimakin sakataren gamayyar kungiyoyin, Malam Suleiman Mu’azu ne yayi wannan kiran, yayin wata ziyara da suka kawo tashar freedom rediyo da safiyar yau.

Ya ce, ya kamata gwamnati ta yi la’akari da halin matsin tattalin arzki  da ake ciki, kafin daukar wannan mataki.

Daya daga cikin mambar kungiyar mai suna Nazifi Shu’aibu, cewa ya yi, ya kamata gwamnati ta dawo da kudin zuwa dubu goma ko biyar ko takwas ko kuma kasa da haka.

Kungiyoyin dai sun ce matukar gwannati ta ki yin la’akari da halin da suke ciki wajen rage kudin, ba kuwa ko shakka da dama daga mambobinsu za su tagayyara.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ganduje ya sanyawa sabuwar gada sunan Sheik Kariballah

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanyawa sabuwar gadar da ake aikin gininta a kan titin kasuwar Rimi sunan shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika Sheikh Kariballah Sheikh Nasiru Kabara.

Gwamna Ganduje ya ayyana radin sunan sabuwar gadar ne a yau, a yayin da ya ke jawabi wajen taron Maukibi da mabiya darikar Kadiriyya ke shiryawa a duk shekara.

Gwamna Ganduje ya ce gwamnati ta yi la’akari da irin gudunmawar da Sheikh Kariballah ke bayarwa wajen daukaka addinin musulunci da kuma hadin kan jama’a, shine ma dalilin da ya sanyawa wannan sabuwar gadar sunanasa.

Gwamna Ganduje ya kuma bukaci Sheikh Kariballah da ya ziyarci gurin da ake aikin ginin gadar don ganewa idanun sa yadda aikin yake wakana tare da sanyawa aikin albarka.

Tarihi dai ya nuna cewa wannan shine karo na 69 da mabiya darikar Kadiriyya ke gudanar da wannan taro.

Continue Reading

Labarai

‘Yan sanda a Kano sun gargadi jama’a kan aikata laifi ranar bikin Maukibi

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano gargadi al’umma, musamman bata gari da suke fakewa da lokacin taron jama’a domin aikata laifukan sara suka, da sauransu.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya rabawa manema labarai a daren yau, ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta shirya tsaf domin kula da shige da fice aranar Asabar mai zuwa da za’a gudanar da bikin maukibin waliyai da mabiya darikar Qadiriyya gabatarwa duk shekara a Kano.

DSP. Kiyawa ya bayyana cewa sunyi shiri na musamman domin zakulo wadanda suke fakewa da irin wadannan taruka su tayar da hankalin jama’a, a don haka suna gargadin al’umma dasu guji yin shigar banza, ko sanya kayan mata ko kuma yin wata shiga wadda ta saba da al’ada ko kuma addinin al’ummar jihar Kano.

Labarai masu alaka:

Rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta sake ceto wani yaro a Anambra

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane

Kazalika rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi shiri na musamman domin dakile masu ta’ammali da miyagun kwayoyi, da sara suka ko kwacen wayoyi da sauran laifuka a yayin gudanar da taron maukibi na bana.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan jihar Kano na sanar da jama’a cewa har yanzu dokar nan tana nan ta haramta yin wani gangami ko zanga-zanga ko wani taron jama’a ba bisa ka’ida ba, kuma duk wanda ya karya wannan doka to babu shakka hukuma zatayi aiki akansa a cewar, kuma anyi hakan ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano a cewar DSP. Kiyawa.

A karshe rundunar ‘yan sandan ta taya al’ummar musulmi murnar zagayowar wannan wata da fatan za’a kammala bukukuwa lafiya.

Labarai masu alaka:

‘Yan film sun karrama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano

Jihar Kano ta sami sabon kwamishinan ‘yan sanda

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.