Labarai
Ma’aikatan man fetur sun yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya
Gamayyar kungiyoyin Ma’aikatan Man Fetur da na iskar Gas ta Najeriya sun yi barazanar shiga yajin aiki, a cikin wata wasika da suka aikewa ministan Man Fetur, Timipre Sylva.
Najeriya na iya fuskantar matsalar karancin mai idan ma’aikatan suka kauracewa aiyukan su yayinda gwamnatin kasar ta dage kan yiwa ma’aikata a bangaren mai rijista a kan hadaden sabon tsarin albashi da ta bullowa ma’aikatan da ke aiki a wurare daban-daban wato IPPIS
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar gamayyar kungiyoyin ma’aikatan sun nuna adawarsu karara ga matakin ofishin akanta janar na tarayya game da rijistar ma’aikatan man fetur din a kan tsarin IPPIS.
Cikin wasikar da suka aikewa ministan man fetur mai dauke da kwanan watan 19 ga watan Yunin 2020, na dauke da sa hannun manyan shugabannin kungiyoyin PENGASSAN da NUPENG, wato Lumumgba Okugbawa da Olawale Afolabi.
Kungiyoyin sun tabbatar da cewa za su tsunduma yajin aiki, matsawar gwamnati ta gaza daukar mataki a kan bukatunsu.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, kungoyin basu bayyana ranar da zasu shiga yajin aikin ba, sai dai suna da yakinin gwamnatin zata duba bukatunsu domin kaucewa matsalar da Najeriya ka iya fadawa game da matsalar man fetur din.
You must be logged in to post a comment Login