Labaran Kano
YakasaiGate: EFCC ta gayyaci tsofaffin kansilolin Kano Municipal
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC shiyyar Kano ta gayyaci tsofaffin kansilolin da suka yi zamani da tsohon shugaban karamar hukumar birni da kewaye Muntari Ishaq Yakasai, a yau Talata.
Wasu daga kansilolin da suka amsa gayyatar hukumar ta EFCC a yau Talata, sun shaidawa Freedom Radio cewar, kudaden da hukumar EFCC ta tambayesu akai, basu da wata masaniya game da su.
Wadanda suke da masaniya kan salwantar kudaden da ake binciken sune tsohon shugaban karamar hukumar da kuma shugaban majalisar kansiloli ta wancan lokacin a cewar tsohon kansila Isma’ila Wada Alhajin Goro.
Karin Labarai:
EFCC ta cafke Muntari Ishaq Yakasai
Muna rokon gwamna Ganduje ya sulhunta Muntari da Sha’aban –Habib Sadam
Dangane da batun zargin badakalar Kasuwar Kofar Wambai tsoffin kansilolin sun ce ba da su akayi watandar kasuwar ba, suma wayar gari sukayi suka ga ana yin ta.
Idan zaku iya tunawa dai a ranar 21 ga watan Fabrairun da ya gabata ne, hukumar ta EFCC ta cafke tsohon shugaban karamar hukumar ta birni kuma kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Kano Alhaji Muntari Ishaq Yakasai.
EFCC ta ce ta cafke Muntari Yakasai ne sakamakon wata takardar korafi da ta samu kan zargin ya karkatar da naira miliyan saba’in da shida mallakar karamar hukumar.
Har ila yau ana zargin Yakasai da gine wani sashe na makarantar Firamare ta Kofar Nasarawa, inda yayi shaguna ya siyar da su aka naira miliyan goma-goma ba bisa ka’ida ba.
Karin Labarai:
Muntari Ishaq ya can-can ci zama kwamishina -Aminu Mai dawa
Siyasa: Muntari bai can-canci zama kwamishina ba –Hamza Darma
You must be logged in to post a comment Login