Coronavirus
Bincike: Masu san’ko na cikin hatsarin kamuwa da cutar Covid-19
Wani binciken masana ya nuna cewa masu san’ko na cikin tsananin hatsarin kamuwa da cutar sarke numfashi ta covid-19.
Binciken wanda jaridar Daily Telegraph dake kasar Ingila ta wallafa a shafinta na internet, ta ce masu dauke da sanko sunfi shiga hatsarin kamuwa da cutar Covid-19 fiye da wadanda basu da shi a fadin duniya.
Shugaban tawagar masu binciken a jami’ar Brown da ke kasar Amurka wato Farfesa Carlos Wambier ya ce sun gudanar da bincike guda biyu a kasar Spain, inda suka gano cewa mafi yawan mutanen da ke kamuwa da cutar maza ne masu sanko.
Nazarin farko da aka gano shine kaso 71% daga marasa lafiya 41 da aka bincika masu dauke da Covid-19 a cikin asibitocin Spain sun kasance maza ne masu sanko
Binciken na biyu, wanda aka wallafa a shafin kwalejin nazarin fata da ke kasar Amurka ya gano cewa kaso 79% daga cikin maza 122 na masu dauke da cutar Coronavirus a asibitocin Madrid masu sanko ne.
Masana ilimin kimiyya sunyi ittifakin cewa sinadarin hormone na mazantaka shi yake kara taimakawa wajen ta’azzara zubewar gashi wanda hakan ne ke bawa cutar Covid-19 damar kai hari ga kwayoyin halittun jikin dan adam.
Wannan na nufin ana iya amfani da magungunan da zasu taimakawa sinadarin hormone wajen kaiwa cutar ta Covid-19 hari wanda kuma hakan zai bawa masu dauke da cutar damar murmurewa a kan lokaci.
You must be logged in to post a comment Login