Coronavirus
Mataimakin gwamnan Bauchi ya warke daga Corona cikin kwana bakwai.
Mataimakin gwamnan Bauchi Baba Tela wanda aka tabbatar ya kamu da cutar Covid-19 a makon da ya gabata ya samu sauki, an kuma sallame shi daga asibiti.
Shugaban hukumar bunkasa lafiya a matakin farko na jihar Bauchi Dakta Rilwanu Muhammad ne ya bayyana hakan ranar Laraba lokacin da yake gabatar da jawabi game da halin da ake ciki kan masu dauke da cutar a jihar.
Idan za a iya tunawa a ranar uku ga watan Yunin 2020 ne aka tabbatar da cewa mataimakin gwamnan na Bauchi ya kamu da cutar Covid-19.
Baba Tela wanda shine shugaban kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar Covid19 da cutar Lassa a jihar Bauchi an killace shi tare da mutanen da ya yi mu’amala da su.
Shugaban hukumar lafiyar a matakin farko na jihar Bauchi y ace an killace mataimakin gwamnan Bauchin har tsawon kwanaki tara kamar yadda gidan talibijin na kasa NTA ya wallafa a shafinsa na internet.
You must be logged in to post a comment Login