Labarai
Covid-19: Ganduje ya nemi kungiyoyi su ri’ka wayar da kan malamai
Gwamnatin Kano ta nemi kungiyar rajin yaki da cutar Corona ta Kano against Covid-19 initiative da ta rika sanya malamai cikin wadanda zata rika yiwa bita akan Corona.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi wannan kiran lokacin yake jawabi a taron bita da kungiyar tare da hadin gwiwar kwamitin kar ta kwana kan Corona ke yiwa wasu ‘yan jaridu a Kano.
Gwamnan ya ce ‘yan jaridu na taka rawar wajen wayar da kan alumma, inda ya ja hankalinsu wajen bawa kansu kariya yayin gudanar da ayyukansu.
Tun farko da yake jawabi, jami’in cibiyar Muhammad Tabi’u ya ce sun bullo da shirin bitar ne da nufin lalubo hanyoyin yaki da annobar Covid-19.
You must be logged in to post a comment Login