ilimi
Gwamnatin Ganduje za ta kaddamar da gidajen da aka gina wa ma’aika
Gwamnatin jihar Kano, za ta kaddamar da gidajen da aka gina domin ma’aikatan gwamnati su mallaka cikin sauki musamman malaman makaranta da za a rika cirar kudin daga albashin su.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya bayyana hakan da yammacin jiya Alhamis lokacin da yake kaddamar da bada shidar daukar Malaman makaranta su dubu daya da dari biyar a dakin taro na Sani Abacha da ke Kofar Mata.
Ganduje, ya kara da cewa gwamnatinsa za ta samar da karin gidajen domin saukaka wa malaman makaranta wajen koyar da dalibai.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma Jagorancin rantsar da sababbin manyan sakatarorin da ya nada a makon nan da muke ciki.
Rahoton: Abba Isah Muhammad
You must be logged in to post a comment Login